Addini Ba Tikitin Shiga Sama Bane

Addini ba tikiti ba ne. Jinin Yesu ne kaɗai izinin shiga sama. Karanta cikakken labari na ceton rai.

HausaTractsForeign Tracts
Download

Addini Ba Tikitin Shiga Sama Bane


Wani mutum, wanda ba zato ba tsammani,
rashin lafiya ta katse masa hanzari na kwazon sa
cikin harkokin rayuwa da kasuwanci
da kuma muhimmin matsayi a Ikilistya
wadda ake darajanta shi,
ya sami zarafin yin tunani.

Da, lokacin yana cikin koshin lafiya
kuma yana bada kokari a cikin hidimomin addini,
ba ya taba tsayawa ya gwada matsayinsa
a gaban Allah ba, balle har ya yi tunanin
inda za ya je bayan ya gama rayuwarsa ta wannan duniya.


Wata rana, wani abokinsa ya zo gaishe shi.
A cikin hirasa sai wannan aboki ya ce da wannan
dankasuwa mara lafiya:

“Na taba zuwa bakin mutuwa sau da yawa,
kuma ba na iya bayyana irin salama da dadin
da ni kan ji a duk lokacin da na ga kamar
ina gaba da saduwa da Allah,
domin ina dogara ga jini mai tamani na Yesu Kristi
a matsayin tikiti ko izini na kadai
na zuwa gaban Allah.”


Sai mara lafiyar ya daga kai ya ce:
“Yan kwanakin nan ina tunani sosai
akan wannan magana.
Ina jin kamar ban nuna kishin addini sosai ba
yadda har zan iya sa begen makoma mai kyau
kamar yadda kake bege ba.
Zan iya bada duk abin da nake da shi
domin in sami irin wannan bege da gaba-gadi irin naka.”


Sai bakon nasa ya ce:
“Ai addini ba tikiti ko kuwa izinin shiga sama bane.”
Addini ba ya taba ba wani salama tsakaninsa da Allah,
ko kuma ya ba shi izinin zuwa gaban Allah ba.

Jinin Yesu Kristi kadai ne ke iya bada
wannan damar zuwa gaban Allah.”


Sai mara lafiyar nan ya nuna mamakin jin wannan zance.
Domin ya saba tunani cewa addini
shine ya fi kome a duniyan nan.
Kuma duk lokacin da mutane suke maganar “tuba”
da “ceto” da kuma “tsarkakewa cikin jinin Kristi”
suna bayani ne kawai bisa ga tunaninsu,
kuma bisa ga irin tasu bangaskiyar
daidai da abin da shi ya dauka cewa shine “addini.”


Abokinsa ya lura da wahalar da yake ciki
— maganar Allah?

Mara lafiyar ya nuna amincewa da murna.
Daga nan sai ya karanta:

“Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna a cikin kasar Masar ...
A fada wa dukan taron Israilawa ...
kowanne namiji ya dauki dan rago ... da ...
Zasu yanka ...
Sa'annan ku debi jinin ku sa a dogaran kofa duka biyu
da bisa kan kofar gidajen da za a ci naman dabbobin ...
A daren, zan ratsa kasar Masar,
in bugi kowane dan fari na kasar na mutum da na dabba.
Zan hukunta gumakan Masar duka, gama ni ne Ubangiji.
Jinin da ke bisa gidajen ku zai nuna inda kuke.
Sa'adda na ga jinin zan tsallake ku,
ba kuma wani bala'in da zai same ku, ya hallaka ku,
a lokacin da zan bugi kasar Masar”
(Fitowa 12:1,2,6,12,13).


Ya yi dan bayani kadan akan ayoyin, ya ce:

“Jinin da aka zubar kuma aka yafa a bisa kofa,
aka dogara gare shi,
shi kadai, shine ya tsiradda dukan wadanda ke cikin gida a wannan daren.
Dukkan wadanda suke karkashin kariyar jinin sun sami tsira;
dukkansu wadanda ba karkashin kariyar jinin ba,
kome kyawun halinsu, sun fada cikin hukunci.”


Sai mara lafiyar nan ya tashi zaune
ya mika hannu ya kama hannun bakon nasa,
a hankali, tare da nuna fahimta, ya ce:

“Ashe, duk yana cikin jinin.
Yanzu ina iya gani sosai cewa
tikiti na samun ceto jinin Kristi ne kadai.”


Akwai mutane da yawa
wadanda suke zaton addini za ya cece su.
Mutane da yawa suna dogara ga adalcinsu
da ayyuka masu zuwa sama.

Allah ya fada cewa jini mai tsarki na Yesu Kristi
(wanda masu zunubi ke dogara da shi)
shine kadai mafakar hukumci mai zuwa.


Jinin Yesu Dansa yana tsarkake mu daga dukkkan zunubi”
(1 Yohanna 1:7)

In ba gama da jini ba kuwa ba gafara”
(Ibraniyawa 9:22)


Hausa-3 “Religion Is Not A Title To Heaven”

📬 Free tracts and biblical counsel available by request. Write:
Word Of Truth, P.O. Box 1126, Kaduna, Nigeria.



Related Products

What is the Truth?

Discover why Jesus’ crucifixion was essential for humanity's salvation as confirmed by prophecies and eyewitness accounts!

Weight of Sin

Explore how God's perfect mercy and justice intersect through the sacrifice of Christ for mankind!

Do you know the humble King?

Discover the humble yet noble journey of God's incarnation as Jesus Christ, offering wisdom, love, and forgiveness!

How to know God

Discover the unique oneness of God and learn how to truly know Him through His infallible word!

Do you know your enemies

Discover your internal enemies and find peace through faith with this inspiring message of salvation!

Karma vs Krupa

Discover how Jesus Christ offers a way out of karma with grace and forgiveness, transforming lives today!

KnowMessiah

Discover if Jesus is the promised Messiah with biblical evidence. Learn how He fulfills ancient prophecies!

Jewish Discovery of a Lifetime

Discover the Jewish quest for atonement and how it leads to finding salvation through Jesus' blood. Explore faith beyond rituals!

Why Believe It?

Explore why the Bible is unshakable and vital through a student's insightful reflection on its enduring impact and divine inspiration. Discover timeless wisdom!

What's Life?

Discover the true meaning of life with Jesus Christ. Find everlasting joy, peace, and fulfillment through faith!

U Turn

Transform your life through repentance and discover the path to eternal peace with Jesus Christ! 🔄✝️

Trapped

Discover how to escape the snares of sin and find freedom through Jesus Christ! 🌿✝️

Those Guilty Stains

Explore how the Bible offers a path from guilt and sin to forgiveness through Jesus Christ! Transform your story today! 🌟✝️

ThisThingWorks

Discover how faith and belief in Jesus Christ can transform your life. This personal story of an intercollegiate boxing champion reveals the power of salvation! 🌟✝️

They Gambled and Lost

Discover life-changing stories of those who gambled with drugs, lost, and found redemption through Jesus Christ. Choose to win! 🌟✝️

Problem with Patty

Explore the fleeting nature of life and embrace eternal joy through Jesus Christ. Discover how to secure a future beyond earthly bounds.

ImHereFor

Discover why living for temporary pleasures can lead to eternal consequences. Find true joy with Christ for a lifetime of happiness. 🌟✝️

GodYouDontKnow

Discover the God you didn't know yet! Explore ancient Athens through Paul's eyes and find faith in Jesus today. Embrace a relationship with the true Creator revealed in Scripture. 🌟🙏

We use cookies

We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy