Hausa7

Akwai bege...ga mutum kamar ni?

$0.04

Labari na gaske na tuba da gafara daga zunubi mai nauyi. Akwai bege ga mai laifi! Ka karanta yadda Kristi ke canza rayuwa — ko kai ma.

0.00 reviews
Login to rate

Quantity

01

Shipping Cost: $0.00

HausaTractsForeign Tracts

Akwai bege...

ga mutum kamar ni?


Wani dare, bayan taron falkaswa a wani babban guri,
sai wani mutum wanda daga ganin shi yana da hatsari
ya nufi mai wa’azin ya tambaye shi:

“Ko za ka yarda ka zo tare da ni a daren yau?
Domin ina so in yi magana da kai.”

“Da farin ciki kuwa,” mai wa’azin ya amsa.

Sai mutumin ya jagoranci tafiya a titunan anguwan
har zuwa gidan sa.
Sai ya bude kofa,
ya ingiza mai wa’azin zuwa ciki,
daga nan sai ya fitar da bindiga.

“Ba zan yi maka illa ba.
Ina so ne in tambaye ka ko kana nufin abin da ka fada da gaske
ne a wa’azin da kayi da daren nan ne,
cewa jinin Yesu Kristi ya wanke mu daga dukan zunuban mu?”

Mai wa’azin ya amsa mishi cewa:

“Kwarai kuwa, haka nike nufi.
Allah ya fada a cikin maganarsa.”

Sai mutumin ya ce:

“Na kashe mutane hudu da wannan bindigan.
Akwai bege ga mutum kamar ni?”

Mai wa’azin ya ce:

“Na sake gaya maka kuma,
idan mutum zai furta ya kuma rabu da dukan zunuban shi,
Allah ya yi alkawari ya yafe shi,
ya kuma wanke shi daga dukan zunuban shi.”
(1 Yohanna 1:7)


Sai mutumin ya ci gaba da cewa:

“A gefe daya na wannan bangon akwai dandali na.
Muna sayar da barasa ga kowa.
A yawancin lokuta, nikan karbi kudin karshe daga mutum
har ya rasa na sayen abinci ga iyalin sa.

A gefen dandalin kuma gidan caca ne da sauran ayyuka na iblis.
Har wani mutum ya taba yin kisan kai domin ya yi asara a wurin.

Akwai bege ga mutum kamar ni?”

Mai wa’azin ya amsa da cewa:

“Allah yana nufin idan ya ce,
‘Jinin Yesu Kristi yana wanke mu daga dukan zunuban mu.’”


“Wani tambaya kuma bayan nan sai ka tafi.
Idan ka bar wannan dandalin, za ka wuce gida na.

Matana tana tare da diya ta mai shekara goma sha daya.
Shekara goma sha uku da suka wuce,
na sadu da wata yarinya mai kyau a New York,
na yi mata karya akan rayuwa na.

Sai ta aure ni, amma bayan da ta tabbatar da gaskiyan,
sai ya raunana mata zuciya.

Tun daga wannan lokaci na sa ya zama mata ‘kiyama a duniya.’
Yanzu ma na fara dukan ta.

A kwanan nan, na mari diyata har na tura ta,
ta fadi a murhu mai zafi,
wanda ya kone ta daga kafada zuwa ga yatsun ta na hannu.

Har hannun ya gurgunce na har abada.
Akwai bege ga mutum kamar ni?”


Mai wa’azin ya kama wannan mutumin,
ya girgiza shi sosai, ya ce:

**“Ka saurare ni da kyau ka ji!
Duk wani irin abin da ka yi a wannan duniya,
maganar Allah tana tsaye:

‘Jinin Yesu Kristi yana wanke mu daga dukan zunuban mu.’

Wannan yana nufin kai!”

Sai mutumin yace:

“Na gode sosai.
Na so in tabbata ne.
Na yarda da kai.
Zan sake zuwa wurin taron ku gobe da daddare kuma.”


Bayan da mai wa’azin ya tafi,
sai mutumin ya fitar da dukan kayan cikin mashayarsa
da kayan cacansa.

Ya farfasa kwalabe da gilashi,
ya kakarya teburan caca da kafafunsu,
ya kone ludo da katin caca a cikin wuta.

Dukan tsawon daren,
ya lalatar da dukan kayan da sukan sa shi zunubi.
Har sai da safiya,
sa’annan ya je ya zauna a kofan gidan — a gajiye.


Daga jin shi ya dawo,
sai matan ta ce wa diyar su:

“Ta je ta ce mishi,
Baba, abincin safe yana shirye domin ka.”

Diyar su ta tafi a hankali zuwa ga baban.
Ta bi a tsorace, ta ce mishi:

“Baba, Mama ta ce abincin safe yayi.”

Sai mutumin, da murmushi, ya ce:

“Kaunatacciyar ‘yata,
Baba baya bukatan abincin safe.”


Diyar sa ta koma da gudu zuwa dakin girkin abinci, ta ce:

“Mama! Baba ya yi mini murmushi!
Ya kuma kirani kaunatacce na!
Bai yi mini ihu ba!”

Maman ta ce:

“Ni ban yarda ba!
Koma ki dai fada mishi abincin safe ya nuna.”

Sai maman ta bi ta a baya.

Da mutumin ya ji su suna zuwa, sai ya yi murmushi, ya ce:

“Zo kusa.”

Da rawan jiki,
matan da diyar suka matso kusa da shi.
A hankali ya sa hannayen shi,
ya rungumi su biyu,
da suka sha wuya a hannun shi.

Sai da hawaye a cike a idanun sa,
sai ya tabbatar musu da cewa:

“Kada ku sake jin tsoro na kuma.
Allah ya ba ku sabon Maigida
da sabon Baba a yau.”


A taro na wannan daren,
matan da diyarsu ma suka bada zuciyan su zuwa ga Kristi.
Suma suka tabbatar da cewa:

“Jinin Yesu Kristi yana wanke mu daga dukan zunuban mu.”
(1 Yohanna 1:7)


Ka Sami Sakon? Zaka furta, ka kuma roki gafaran zunuban ka yanzu?
Ka kuma bada ranka zuwa ga Kristi?
Roki Allah ya yafe maka.
Akwai bege domin wani kamar ka!


Hausa–7 “Is There Hope For A Man Like Me?”

Free tracts and biblical counsel available by request.
Write: Word Of Truth
P.O. Box 1126, Kaduna, Nigeria

Related Products

What is the Truth?

What is the Truth?

The Weight of SIN

The Weight of SIN

Do you know the Humble King?

Do you know the Humble King?

How To Know GOD

How To Know GOD

Do you know your ENEMIES?

Do you know your ENEMIES?

KARMA versus KRUPA

KARMA versus KRUPA

Do You Know the Messiah?

Do You Know the Messiah?

Jewish Discovery of a Lifetime

Jewish Discovery of a Lifetime

Why Believe It?

Why Believe It?

When should you think about CHRIST?

When should you think about CHRIST?

When God Knows Your Your Name

When God Knows Your Your Name

What's Life?

What's Life?

U-Turn

U-Turn

Trapped!

Trapped!

Those Guilty Stains

Those Guilty Stains

THIS THING WORKS!

THIS THING WORKS!

They Gambled and Lost! Will You?

They Gambled and Lost! Will You?

The Problem with Patty

The Problem with Patty

I’m Here for a Good Time

I’m Here for a Good Time

The You Don't Know Yet

The You Don't Know Yet

We use cookies

We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy