
Akwai bege...ga mutum kamar ni?
$0.04Labari na gaske na tuba da gafara daga zunubi mai nauyi. Akwai bege ga mai laifi! Ka karanta yadda Kristi ke canza rayuwa โ ko kai ma.
Quantity
Shipping Cost: $0.00
We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy
$0.04
Wani dare, bayan taron falkaswa a wani babban guri,
sai wani mutum wanda daga ganin shi yana da hatsari
ya nufi mai waโazin ya tambaye shi:
โKo za ka yarda ka zo tare da ni a daren yau?
Domin ina so in yi magana da kai.โ
โDa farin ciki kuwa,โ mai waโazin ya amsa.
Sai mutumin ya jagoranci tafiya a titunan anguwan
har zuwa gidan sa.
Sai ya bude kofa,
ya ingiza mai waโazin zuwa ciki,
daga nan sai ya fitar da bindiga.
โBa zan yi maka illa ba.
Ina so ne in tambaye ka ko kana nufin abin da ka fada da gaske
ne a waโazin da kayi da daren nan ne,
cewaย jinin Yesu Kristi ya wanke mu daga dukan zunuban mu?โ
Mai waโazin ya amsa mishi cewa:
โKwarai kuwa, haka nike nufi.
Allah ya fada a cikin maganarsa.โ
Sai mutumin ya ce:
โNa kashe mutane hudu da wannan bindigan.
Akwai bege ga mutum kamar ni?โ
Mai waโazin ya ce:
โNa sake gaya maka kuma,
idan mutum zai furta ya kuma rabu da dukan zunuban shi,
Allah ya yi alkawari ya yafe shi,
ya kuma wanke shi daga dukan zunuban shi.โ
(1 Yohanna 1:7)
Sai mutumin ya ci gaba da cewa:
โA gefe daya na wannan bangon akwai dandali na.
Muna sayar da barasa ga kowa.
A yawancin lokuta, nikan karbi kudin karshe daga mutum
har ya rasa na sayen abinci ga iyalin sa.A gefen dandalin kuma gidan caca ne da sauran ayyuka na iblis.
Har wani mutum ya taba yin kisan kai domin ya yi asara a wurin.Akwai bege ga mutum kamar ni?โ
Mai waโazin ya amsa da cewa:
โAllah yana nufin idan ya ce,
โJinin Yesu Kristi yana wanke mu daga dukan zunuban mu.โโ
โWani tambaya kuma bayan nan sai ka tafi.
Idan ka bar wannan dandalin, za ka wuce gida na.Matana tana tare da diya ta mai shekara goma sha daya.
Shekara goma sha uku da suka wuce,
na sadu da wata yarinya mai kyau a New York,
na yi mata karya akan rayuwa na.Sai ta aure ni, amma bayan da ta tabbatar da gaskiyan,
sai ya raunana mata zuciya.Tun daga wannan lokaci na sa ya zama mata โkiyama a duniya.โ
Yanzu ma na fara dukan ta.A kwanan nan, na mari diyata har na tura ta,
ta fadi a murhu mai zafi,
wanda ya kone ta daga kafada zuwa ga yatsun ta na hannu.Har hannun ya gurgunce na har abada.
Akwai bege ga mutum kamar ni?โ
Mai waโazin ya kama wannan mutumin,
ya girgiza shi sosai, ya ce:
**โKa saurare ni da kyau ka ji!
Duk wani irin abin da ka yi a wannan duniya,
maganar Allah tana tsaye:โJinin Yesu Kristi yana wanke mu daga dukan zunuban mu.โ
Wannan yana nufinย kai!โ
Sai mutumin yace:
โNa gode sosai.
Na so in tabbata ne.
Na yarda da kai.
Zan sake zuwa wurin taron ku gobe da daddare kuma.โ
Bayan da mai waโazin ya tafi,
sai mutumin ya fitar daย dukan kayan cikin mashayarsa
daย kayan cacansa.
Ya farfasaย kwalabe da gilashi,
ya kakaryaย teburan caca da kafafunsu,
ya koneย ludo da katin caca a cikin wuta.
Dukan tsawon daren,
ya lalatar da dukan kayan da sukan sa shi zunubi.
Har sai da safiya,
saโannan ya je ya zauna a kofan gidan โย a gajiye.
Daga jin shi ya dawo,
sai matan ta ce wa diyar su:
โTa je ta ce mishi,
Baba, abincin safe yana shirye domin ka.โ
Diyar su ta tafi a hankali zuwa ga baban.
Ta bi a tsorace, ta ce mishi:
โBaba, Mama ta ce abincin safe yayi.โ
Sai mutumin, da murmushi, ya ce:
โKaunatacciyar โyata,
Baba baya bukatan abincin safe.โ
Diyar sa ta koma da gudu zuwa dakin girkin abinci, ta ce:
โMama! Baba ya yi mini murmushi!
Ya kuma kirani kaunatacce na!
Bai yi mini ihu ba!โ
Maman ta ce:
โNi ban yarda ba!
Koma ki dai fada mishi abincin safe ya nuna.โ
Sai maman ta bi ta a baya.
Da mutumin ya ji su suna zuwa, sai ya yi murmushi, ya ce:
โZo kusa.โ
Da rawan jiki,
matan da diyar suka matso kusa da shi.
A hankali ya sa hannayen shi,
ya rungumi su biyu,
da suka sha wuya a hannun shi.
Sai da hawaye a cike a idanun sa,
sai ya tabbatar musu da cewa:
โKada ku sake jin tsoro na kuma.
Allah ya ba kuย sabon Maigida
daย sabon Babaย a yau.โ
A taro na wannan daren,
matan da diyarsu ma suka bada zuciyan su zuwa ga Kristi.
Suma suka tabbatar da cewa:
โJinin Yesu Kristi yana wanke mu daga dukan zunuban mu.โ
(1 Yohanna 1:7)
Ka Sami Sakon? Zaka furta, ka kuma roki gafaran zunuban ka yanzu?
Ka kuma bada ranka zuwa ga Kristi?
Roki Allah ya yafe maka.
Akwai bege domin wani kamar ka!
Free tracts and biblical counsel available by request.
Write: Word Of Truth
P.O. Box 1126, Kaduna, Nigeria

Labari na gaske na tuba da gafara daga zunubi mai nauyi. Akwai bege ga mai laifi! Ka karanta yadda Kristi ke canza rayuwa โ ko kai ma.
Quantity
Shipping Cost: $0.00