AN MAYA HAIFUWARKA?

Kada ka yi sakaci: idan ba a sake haifuwarka ba, ba za ka ga mulkin Allah ba. Karanta yadda zaka sami sabuwar rayuwa cikin Kristi.

HausaTractsForeign Tracts
Download

AN MAYA HAIFUWARKA?


Dukkan wanda yake so ya je sama gidan Allah

“dole ne a sake haifuwarsa.”

Ubangiji Yesu ya ce:

“Hakika, hakika ina fada maku, in ba a sake haifuwar mutum ba,

ba za ya iya shiga cikin mulkin Allah ba.” (Yohanna 3:3)

Kamar yadda ka sami rai na jiki

lokacin da aka haife ka cikin duniyar nan,

haka nan dole a sake haifuwarka kafin ka sami

rai na ruhaniya — Ruhun Allah —

domin ka ji dadin abubuwa na Allah da kuma sama.


Ka kasa kunne ga wadannan kalmomi na Yesu Kristi:


“Hakika, ina gaya maka,

in ba an haifi mutum ta ruwa da ta Ruhu ba,

ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.

Abin da mutum ya haifa mutum ne,

abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne.

Kaka ka yi mamaki domin na ce maka,

‘Dole a sake haifarka.’”

(Yohanna 3:5–7)

Maya haifuwa — haifuwa ce ta ruhaniya.

Lokacin da aka haife mu cikin wannan duniya,

mun yi gadon halin zunubi na iyayenmu.

A cikin Littafi Mai Tsarki an bayyana cewa

mun “mutu cikin zunubanmu” (Afisawa 2:1).

A cikin irin wannan hali

ba za mu taba iya shiga mulkin Allah ba.

Dole ne sai mun canja.

“Dole a sake haifuwarka.”


Wannan kalami ya fito daga bakin Dan Allah.

Sabuwar haifuwa ta Ruhun Allah wajibi ce

idan har mutum yana so ya sami ruhaniya

kuma ya dace domin zuwa gaban Allah.


Mutum ba ya iya bada wannan sabuwar haifuwa.

Haka kuma ba ta samuwa ta wurin ayyuka na addini

ko kuwa a wurin shugabannin addini.


Nikodimu — wanda Yesu ya ce wa

“Dole a sake haifuwarka” —

shi Bafarise ne mai tsananin ra'ayin addini,

basarake ne na Yahudawa,

kuma Ubangidan wasu ne a cikin Isra'ila.

Duk da haka yana bukatar a maya haifuwarsa.

Ba ya cancanci shiga mulkin Allah ba.


Cikin mamaki sai ya tambayi Ubangiji ya ce,

“Ta yaya wannan zai faru?”

Kalmomin Ubangiji Yesu suka sauko da shi

kasa daga bisa babban mukamin addini da ya ke.

Nikodimu ya gane cewa

shi mai zunubi ne, abin tausayi,

wanda ba shi da rabo cikin mulkin Allah.


Yanzu ya shirya jin abu na biyu

game da wani aiki wanda dole ne wani ya yi dominsa.


“Kamar yadda Musa ya daga macijin nan a jeji,

haka kuma dole ne a daga Dan Mutum.”

(Yohanna 3:14–15)

Za a giciye Yesu saboda zunuban masu zunubi

domin dukkan wanda ya bada gaskiya gare shi

a matsayin Mai cetonsa,

za ya sami rai na har abada.


Ruhun Allah ne yake yin aikin sabunta haifuwar

a cikin zukatan mutanen da suke gaskanta

da Mai Ceto wanda aka giciye

kuma suka karbi rai na Ruhu da zuciya daya.


Wannan ita ce ainihin ma'anar

“maya haifuwa da ruwa da kuma Ruhu.”


Lokacin da maganar Allah,

ga halin kaka-ni-ka-yi na mutum

kuma a matsayin fansar zunubi cikin giciyen Kristi,

ta soki zuciyar mutum cikin ikon Ruhu Mai Tsarki,

kuma ya gaskanta ya karya cikin zuciya —

to an maya-haifuwarsa ke nan ta wurin Ruhun Allah,

kuma an cece shi.


Ya sami sabuwar rayuwa ta ruhaniya,

ya zama wanda kwa

“tarayya da Allah wajen dabi’arsa” (2 Bitrus 1:4).

Kuma ya zama sabuwar halitta cikin Kristi.


“Tsofaffin al’amura sun shude ...

kome ya zama sabo.”

(2 Korintiyawa 5:17)

Wannan shi ne abin da wanda aka haifa daga Allah

za ya dandana.


Wadansu suna zato cewa

“haifuwa ta ruwa da Ruhu”

suna nufin baptisma ta ruwa.

Amma maganar Allah ta nuna a sarari cewa

maganar Allah, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki,

tana canja mutum.


(Afisawa 5:26) — “ya kawo mu ta ruwa ta wurin kalma”

(Yakub 1:18) — “Bisa nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya”

(1 Bitrus 1:23) — “Gama sake haifarka aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba,

sai marar lalacewa, wato ta maganar Allah rayayya, kuma dawammamiya.”

(Yohanna 1:12–13) — “wadanda suka karbi Kristi kuma suka bada gaskiya

ga sunansa sun zama ya’yan Allah kuma haifaffu daga Allah.”

Babbar tambayar ita ce:

An maya-haifuwarka?

Akwai canji cikin rayuwarka?

Kana da rai cikin Kristi

ko kuwa kana masa bauta da baki ne kawai?


Idan kai mai addini ne

amma baka taba samun maya haifuwa

ko kuwa sakéwa ta ruhaniya a cikin ranka ba,

to har yanzu kai matacce ne cikin zunubi,

babu ruhaniya a cikinka.


KIYAYE TADODI ko kuwa ka'idodin addini

baya kawo canji na ruhaniya.


IDAN BA A MAYA HAIFUWAR MUTUM BA,

BA ZA YA GA MULKIN ALLAH BA.


Kada ka yi sakaci da wannan muhimmiyar magana.


Idan an haife ka sau daya kawai,

dole ne ka mutu sau biyu.

Amma idan an haife ka sau biyu,

zaka mutu sau daya kawai —

sai dai ko idan Ubangiji Yesu ya zo

kafin ka ratsa mutuwa.

(Ruya ta Yohanna 2:11; 20:6;

1 Tassalonikawa 4:17).

Ga dukkan wadanda ba a taba maya haifuwarsu ba,

akwai mutuwa ta biyu,

wato rabuwa ta har abada da Allah,

da rayuwa cikin gidan wuta har abada abadin.


Amma ga dukkan wadanda an maya haifuwarsu

ta wurin Ruhu Mai Tsarki,

akwai rabo ko rayuwa ta har abada

tare da Ubangiji a cikin gidansa.


Wanne ka zaba a cikin rayuwar nan iri biyu?


— marubuci: R.K. Campbell


Hausa-1 “Have You Been Born Again?”

Free tracts and biblical counsel available by request. Write:

Word Of Truth, P.O. Box 1126, Kaduna, Nigeria.

Related Products

What is the Truth?

Discover why Jesus’ crucifixion was essential for humanity's salvation as confirmed by prophecies and eyewitness accounts!

Weight of Sin

Explore how God's perfect mercy and justice intersect through the sacrifice of Christ for mankind!

Do you know the humble King?

Discover the humble yet noble journey of God's incarnation as Jesus Christ, offering wisdom, love, and forgiveness!

How to know God

Discover the unique oneness of God and learn how to truly know Him through His infallible word!

Do you know your enemies

Discover your internal enemies and find peace through faith with this inspiring message of salvation!

Karma vs Krupa

Discover how Jesus Christ offers a way out of karma with grace and forgiveness, transforming lives today!

KnowMessiah

Discover if Jesus is the promised Messiah with biblical evidence. Learn how He fulfills ancient prophecies!

Jewish Discovery of a Lifetime

Discover the Jewish quest for atonement and how it leads to finding salvation through Jesus' blood. Explore faith beyond rituals!

Why Believe It?

Explore why the Bible is unshakable and vital through a student's insightful reflection on its enduring impact and divine inspiration. Discover timeless wisdom!

What's Life?

Discover the true meaning of life with Jesus Christ. Find everlasting joy, peace, and fulfillment through faith!

U Turn

Transform your life through repentance and discover the path to eternal peace with Jesus Christ! 🔄✝️

Trapped

Discover how to escape the snares of sin and find freedom through Jesus Christ! 🌿✝️

Those Guilty Stains

Explore how the Bible offers a path from guilt and sin to forgiveness through Jesus Christ! Transform your story today! 🌟✝️

ThisThingWorks

Discover how faith and belief in Jesus Christ can transform your life. This personal story of an intercollegiate boxing champion reveals the power of salvation! 🌟✝️

They Gambled and Lost

Discover life-changing stories of those who gambled with drugs, lost, and found redemption through Jesus Christ. Choose to win! 🌟✝️

Problem with Patty

Explore the fleeting nature of life and embrace eternal joy through Jesus Christ. Discover how to secure a future beyond earthly bounds.

ImHereFor

Discover why living for temporary pleasures can lead to eternal consequences. Find true joy with Christ for a lifetime of happiness. 🌟✝️

GodYouDontKnow

Discover the God you didn't know yet! Explore ancient Athens through Paul's eyes and find faith in Jesus today. Embrace a relationship with the true Creator revealed in Scripture. 🌟🙏

We use cookies

We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy