
We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy
$0.04
Dukkan wanda yake so ya je sama gidan Allah
ādole ne a sake haifuwarsa.ā
Ubangiji Yesu ya ce:
āHakika, hakika ina fada maku, in ba a sake haifuwar mutum ba,
ba za ya iya shiga cikin mulkin Allah ba.ā (Yohanna 3:3)
Kamar yadda ka sami rai na jiki
lokacin da aka haife ka cikin duniyar nan,
haka nan dole a sake haifuwarka kafin ka sami
rai na ruhaniya ā Ruhun Allah ā
domin ka ji dadin abubuwa na Allah da kuma sama.
Ka kasa kunne ga wadannan kalmomi na Yesu Kristi:
āHakika, ina gaya maka,
in ba an haifi mutum ta ruwa da ta Ruhu ba,
ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.
Abin da mutum ya haifa mutum ne,
abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne.
Kaka ka yi mamaki domin na ce maka,
āDole a sake haifarka.āā
(Yohanna 3:5ā7)
Maya haifuwa ā haifuwa ce ta ruhaniya.
Lokacin da aka haife mu cikin wannan duniya,
mun yi gadon halin zunubi na iyayenmu.
A cikin Littafi Mai Tsarki an bayyana cewa
mun āmutu cikin zunubanmuā (Afisawa 2:1).
A cikin irin wannan hali
ba za mu taba iya shiga mulkin Allah ba.
Dole ne sai mun canja.
āDole a sake haifuwarka.ā
Wannan kalami ya fito daga bakin Dan Allah.
Sabuwar haifuwa ta Ruhun Allah wajibi ce
idan har mutum yana so ya sami ruhaniya
kuma ya dace domin zuwa gaban Allah.
Mutum ba ya iya bada wannan sabuwar haifuwa.
Haka kuma ba ta samuwa ta wurin ayyuka na addini
ko kuwa a wurin shugabannin addini.
Nikodimu ā wanda Yesu ya ce wa
āDole a sake haifuwarkaā ā
shi Bafarise ne mai tsananin ra'ayin addini,
basarake ne na Yahudawa,
kuma Ubangidan wasu ne a cikin Isra'ila.
Duk da haka yana bukatar a maya haifuwarsa.
Ba ya cancanci shiga mulkin Allah ba.
Cikin mamaki sai ya tambayi Ubangiji ya ce,
āTa yaya wannan zai faru?ā
Kalmomin Ubangiji Yesu suka sauko da shi
kasa daga bisa babban mukamin addini da ya ke.
Nikodimu ya gane cewa
shi mai zunubi ne, abin tausayi,
wanda ba shi da rabo cikin mulkin Allah.
Yanzu ya shirya jin abu na biyu
game da wani aiki wanda dole ne wani ya yi dominsa.
āKamar yadda Musa ya daga macijin nan a jeji,
haka kuma dole ne a daga Dan Mutum.ā
(Yohanna 3:14ā15)
Za a giciye Yesu saboda zunuban masu zunubi
domin dukkan wanda ya bada gaskiya gare shi
a matsayin Mai cetonsa,
za ya sami rai na har abada.
Ruhun Allah ne yake yin aikin sabunta haifuwar
a cikin zukatan mutanen da suke gaskanta
da Mai Ceto wanda aka giciye
kuma suka karbi rai na Ruhu da zuciya daya.
Wannan ita ce ainihin ma'anar
āmaya haifuwa da ruwa da kuma Ruhu.ā
Lokacin da maganar Allah,
ga halin kaka-ni-ka-yi na mutum
kuma a matsayin fansar zunubi cikin giciyen Kristi,
ta soki zuciyar mutum cikin ikon Ruhu Mai Tsarki,
kuma ya gaskanta ya karya cikin zuciya ā
to an maya-haifuwarsa ke nan ta wurin Ruhun Allah,
kuma an cece shi.
Ya sami sabuwar rayuwa ta ruhaniya,
ya zama wanda kwa
ātarayya da Allah wajen dabiāarsaā (2 Bitrus 1:4).
Kuma ya zama sabuwar halitta cikin Kristi.
āTsofaffin alāamura sun shude ...
kome ya zama sabo.ā
(2 Korintiyawa 5:17)
Wannan shi ne abin da wanda aka haifa daga Allah
za ya dandana.
Wadansu suna zato cewa
āhaifuwa ta ruwa da Ruhuā
suna nufin baptisma ta ruwa.
Amma maganar Allah ta nuna a sarari cewa
maganar Allah, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki,
tana canja mutum.
(Afisawa 5:26) ā āya kawo mu ta ruwa ta wurin kalmaā
(Yakub 1:18) ā āBisa nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiyaā
(1 Bitrus 1:23) ā āGama sake haifarka aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba,
sai marar lalacewa, wato ta maganar Allah rayayya, kuma dawammamiya.ā
(Yohanna 1:12ā13) ā āwadanda suka karbi Kristi kuma suka bada gaskiya
ga sunansa sun zama yaāyan Allah kuma haifaffu daga Allah.ā
Babbar tambayar ita ce:
An maya-haifuwarka?
Akwai canji cikin rayuwarka?
Kana da rai cikin Kristi
ko kuwa kana masa bauta da baki ne kawai?
Idan kai mai addini ne
amma baka taba samun maya haifuwa
ko kuwa sakƩwa ta ruhaniya a cikin ranka ba,
to har yanzu kai matacce ne cikin zunubi,
babu ruhaniya a cikinka.
KIYAYE TADODI ko kuwa ka'idodin addini
baya kawo canji na ruhaniya.
IDAN BA A MAYA HAIFUWAR MUTUM BA,
BA ZA YA GA MULKIN ALLAH BA.
Kada ka yi sakaci da wannan muhimmiyar magana.
Idan an haife ka sau daya kawai,
dole ne ka mutu sau biyu.
Amma idan an haife ka sau biyu,
zaka mutu sau daya kawai ā
sai dai ko idan Ubangiji Yesu ya zo
kafin ka ratsa mutuwa.
(Ruya ta Yohanna 2:11; 20:6;
1 Tassalonikawa 4:17).
Ga dukkan wadanda ba a taba maya haifuwarsu ba,
akwai mutuwa ta biyu,
wato rabuwa ta har abada da Allah,
da rayuwa cikin gidan wuta har abada abadin.
Amma ga dukkan wadanda an maya haifuwarsu
ta wurin Ruhu Mai Tsarki,
akwai rabo ko rayuwa ta har abada
tare da Ubangiji a cikin gidansa.
Wanne ka zaba a cikin rayuwar nan iri biyu?
ā marubuci: R.K. Campbell
Hausa-1 āHave You Been Born Again?ā
Free tracts and biblical counsel available by request. Write:
Word Of Truth, P.O. Box 1126, Kaduna, Nigeria.

Kada ka yi sakaci: idan ba a sake haifuwarka ba, ba za ka ga mulkin Allah ba. Karanta yadda zaka sami sabuwar rayuwa cikin Kristi.
Quantity
Shipping Cost: $0.00