Hausa4

Bayan Mutuwa, Ina Zaka Dauwama?

$0.04

Sakon ceto daga zunubi da hukunci, gayyata zuwa gafara da rai madawwami ta wurin Yesu Kristi. Ka karanta kafin lokaci ya kure.

0.00 reviews
Login to rate

Quantity

01

Shipping Cost: $0.00

HausaTractsForeign Tracts

Bayan Mutuwa, Ina Zaka Dauwama?


Wannan tambaya tana da sukan zuciya.

Mai yiwuwa ne kana ji da lafiya da karfin jiki,

kuma kana gani kamar kana da sauran kwanaki da yawa a duniya.

Idan ba haka ba ne fa?

Idan mutuwa tana kurkusa fiye da yadda kake tunani fa?


Wani mai arziki ya taba fada a ransa ya ce,

“Ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru.

Bari in huta, in yi ta ci, ni yi ta sha,”

ya da daren nan ana bidar ranka a gare ka” (Luka 12:20).


Mai yiwuwa ne wannan mai arziki gabansa ya fadi da jin cewa

ya rage masu ‘yan awoyi kawai ya bar duniyar.

Ba ka san lokacin da zaka mutu ba.


Ka Shirya Tun Yanzu

Kristi yana kwankwasawa a kofar zuciyarka,

yana jira ka bude masa:

Ya ce, “Yau ce ranar ceto” (2 Korintiyawa 6:2).

“Kada ka yi farahiya saboda gobe domin baka san abin da gobe zata kawo ba” (Misalai 27:1).


Ka karbi kyautar ceto da Allah yake baka yanzu —

a yadda kake.


Ana Lura Da Yadda Kake Rayuwa

Allah yana lura sosai da dukkan abin da ke tattare da rayuwarka,

kuma “zai tone al’amuran da ke boye a duhu,

ya kuma bayyana nufin zukata” (1 Korintiyawa 4:5).


Ranar da za a tone kowanne boyayyen abu

na tunani da ayyuka a gaban Allah,

akwai ban razana.


Ba ka daukaka shi ba a cikin tunani da ayyuka.

Ba ka gode masa ba yadda ya kamata.

Ka yi ta rayuwa don kanka,

bisa ga taka sha’awa da shiri,

ba tare da ka nemi nufin Allah ba.


Yaya za ka sadu da Allah a cikin wannan rana ta shari’a,

ba tare da mai cetonka ba?


Ranar Shari’a Tana Zuwa

“Sa’annan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda ke zaune a kai ...

Sai na ga matattu, manya da yara, tsaitsaye kursiyin,

aka kuma bude littattafai.”

(Ruya ta Yohanna 20:11,12)

Ba za a yi maka shari’a bisa abin da ka yi tunani game da kanka ba,

haka nan kuma ba bisa abin da wasu suke tunaninka ba.


Za a shari’anta maka bisa abin da Allah da kansa ya rubuta cikin wadannan littattafai.


“Aka kwa yi wa matattu shari’a bisa ga abin da ke rubuce cikin littattafan,

gwargwadon aikin da suka yi.”

(Ruya ta Yohanna 20:12)

Allah yana ganin duk wani tunani da wata manufa da ke cikin zuciyar mutum.

Ya san kowanne tunani na asiri da kuma duk wani abin da aka aikata a boye.


“Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai ba,

sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.”

(Ruya ta Yohanna 20:15)

Babu wanda zai tsere wa shari’a,

sai ko wadanda aka sami sunayensu a cikin Littafin Rai.


Amma Ka Dakata!

Ka yi tunani wani dan lokaci kadan akan

abin da Yesu Kristi ya yi domin ka a bisa giciye.

“Domin Almasihu ma ya mutu sau daya tak ba kari,

domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci,

domin ya kai mu ga Allah.”

(1 Bitrus 3:18)

“Shi kansa ya dauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume.”

(1 Bitrus 2:24)


“Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa.

Hukuncin da ya wajaba a kanmu.”

(Ishaya 53:6)

“Shi Almasihu ma, da aka mika shi hadaya sau daya tak,

domin ya dauke zunuban mutane da yawa.”

(Ibraniyawa 9:28)

“Jinin Yesu Dansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.”

(1 Yohanna 1:7)

Kauna

“Ta haka kauna take, wato ba mu bane muka kaunaci Allah ba,

sai dai shi ne ya kaunace mu, ya aiko Dansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.” (1 Yohanna 4:10)

Ka yi tunanin abin da Yesu Kristi ya bayar.

Ya hakura da daukakarsa, domin ya sha wahala a bisa giciye,

domin mu kubuta daga shari’a kuma mu zauna a sama tare da shi har abada.


“Ba kaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum ya ba da ransa saboda aminansa.”

(Yohanna 15:13)

“Yadda muka san kauna ke nan , wato ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu.”

(1 Yohanna 3:16)

A shirye yake ya karbe ka

ya kuma gafarta maka dukkan zunubanka

idan har ka furta su.


Ka zo gare shi da kowanne irin hali kake da shi, ko kuma kake ciki.


Ka saurara ka ji ga shi yana kiranka, yana cewa:


“Ku zo gare ni, dukanku da ku ke wahala,

masu nauyin kaya kuma, ni kuwa zan baku hutawa.”

(Matta 11:28)

Ka zo yanzu.

Idan ka bari sai gobe, ai yiwuwa ne ka makara.


Hausa–4 “Where Will You Spend Eternity?”

Free tracts and biblical counsel available by request. Write:

Word Of Truth

P.O. Box 1126, Kaduna, Nigeria.

Related Products

What is the Truth?

What is the Truth?

The Weight of SIN

The Weight of SIN

Do you know the Humble King?

Do you know the Humble King?

How To Know GOD

How To Know GOD

Do you know your ENEMIES?

Do you know your ENEMIES?

KARMA versus KRUPA

KARMA versus KRUPA

Do You Know the Messiah?

Do You Know the Messiah?

Jewish Discovery of a Lifetime

Jewish Discovery of a Lifetime

Why Believe It?

Why Believe It?

When should you think about CHRIST?

When should you think about CHRIST?

When God Knows Your Your Name

When God Knows Your Your Name

What's Life?

What's Life?

U-Turn

U-Turn

Trapped!

Trapped!

Those Guilty Stains

Those Guilty Stains

THIS THING WORKS!

THIS THING WORKS!

They Gambled and Lost! Will You?

They Gambled and Lost! Will You?

The Problem with Patty

The Problem with Patty

I’m Here for a Good Time

I’m Here for a Good Time

The You Don't Know Yet

The You Don't Know Yet

We use cookies

We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy