
Bayan Mutuwa, Ina Zaka Dauwama?
$0.04Sakon ceto daga zunubi da hukunci, gayyata zuwa gafara da rai madawwami ta wurin Yesu Kristi. Ka karanta kafin lokaci ya kure.
Quantity
Shipping Cost: $0.00
We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy
Wannan tambaya tana da sukan zuciya.
Mai yiwuwa ne kana ji da lafiya da karfin jiki,
kuma kana gani kamar kana da sauran kwanaki da yawa a duniya.
Idan ba haka ba ne fa?
Idan mutuwa tana kurkusa fiye da yadda kake tunani fa?
Wani mai arziki ya taba fada a ransa ya ce,
โIna da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru.
Bari in huta, in yi ta ci, ni yi ta sha,โ
ya da daren nan ana bidar ranka a gare kaโ (Luka 12:20).
Mai yiwuwa ne wannan mai arziki gabansa ya fadi da jin cewa
ya rage masu โyan awoyi kawai ya bar duniyar.
Ba ka san lokacin da zaka mutu ba.
Kristi yana kwankwasawa a kofar zuciyarka,
yana jira ka bude masa:
Ya ce, โYau ce ranar cetoโ (2 Korintiyawa 6:2).
โKada ka yi farahiya saboda gobe domin baka san abin da gobe zata kawo baโ (Misalai 27:1).
Ka karbi kyautar ceto da Allah yake baka yanzu โ
a yadda kake.
Allah yana lura sosai da dukkan abin da ke tattare da rayuwarka,
kuma โzai tone alโamuran da ke boye a duhu,
ya kuma bayyana nufin zukataโ (1 Korintiyawa 4:5).
Ranar da za a tone kowanne boyayyen abu
na tunani da ayyuka a gaban Allah,
akwai ban razana.
Ba ka daukaka shi ba a cikin tunani da ayyuka.
Ba ka gode masa ba yadda ya kamata.
Ka yi ta rayuwa don kanka,
bisa ga taka shaโawa da shiri,
ba tare da ka nemi nufin Allah ba.
Yaya za ka sadu da Allah a cikin wannan rana ta shariโa,
ba tare da mai cetonka ba?
โSaโannan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda ke zaune a kai ...
Sai na ga matattu, manya da yara, tsaitsaye kursiyin,
aka kuma bude littattafai.โ
(Ruya ta Yohanna 20:11,12)
Ba za a yi maka shariโa bisa abin da ka yi tunani game da kanka ba,
haka nan kuma ba bisa abin da wasu suke tunaninka ba.
Za a shariโanta maka bisa abin da Allah da kansa ya rubuta cikin wadannan littattafai.
โAka kwa yi wa matattu shariโa bisa ga abin da ke rubuce cikin littattafan,
gwargwadon aikin da suka yi.โ
(Ruya ta Yohanna 20:12)
Allah yana ganin duk wani tunani da wata manufa da ke cikin zuciyar mutum.
Ya san kowanne tunani na asiri da kuma duk wani abin da aka aikata a boye.
โDuk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai ba,
sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.โ
(Ruya ta Yohanna 20:15)
Babu wanda zai tsere wa shariโa,
sai ko wadanda aka sami sunayensu a cikin Littafin Rai.
Ka yi tunani wani dan lokaci kadan akan
abin da Yesu Kristi ya yi domin ka a bisa giciye.
โDomin Almasihu ma ya mutu sau daya tak ba kari,
domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci,
domin ya kai mu ga Allah.โ
(1 Bitrus 3:18)
โShi kansa ya dauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume.โ
(1 Bitrus 2:24)
โUbangiji ya sa hukunci ya auko a kansa.
Hukuncin da ya wajaba a kanmu.โ
(Ishaya 53:6)
โShi Almasihu ma, da aka mika shi hadaya sau daya tak,
domin ya dauke zunuban mutane da yawa.โ
(Ibraniyawa 9:28)
โJinin Yesu Dansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.โ
(1 Yohanna 1:7)
โTa haka kauna take, wato ba mu bane muka kaunaci Allah ba,
sai dai shi ne ya kaunace mu, ya aiko Dansa, hadayar sulhu saboda a gafarta zunubanmu.โ (1 Yohanna 4:10)
Ka yi tunanin abin da Yesu Kristi ya bayar.
Ya hakura da daukakarsa, domin ya sha wahala a bisa giciye,
domin mu kubuta daga shariโa kuma mu zauna a sama tare da shi har abada.
โBa kaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum ya ba da ransa saboda aminansa.โ
(Yohanna 15:13)
โYadda muka san kauna ke nan , wato ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu.โ
(1 Yohanna 3:16)
A shirye yake ya karbe ka
ya kuma gafarta maka dukkan zunubanka
idan har ka furta su.
Ka zo gare shi da kowanne irin hali kake da shi, ko kuma kake ciki.
Ka saurara ka ji ga shi yana kiranka, yana cewa:
โKu zo gare ni, dukanku da ku ke wahala,
masu nauyin kaya kuma, ni kuwa zan baku hutawa.โ
(Matta 11:28)
Ka zo yanzu.
Idan ka bari sai gobe, ai yiwuwa ne ka makara.
Hausaโ4 โWhere Will You Spend Eternity?โ
Free tracts and biblical counsel available by request. Write:
Word Of Truth
P.O. Box 1126, Kaduna, Nigeria.
$0.04

Sakon ceto daga zunubi da hukunci, gayyata zuwa gafara da rai madawwami ta wurin Yesu Kristi. Ka karanta kafin lokaci ya kure.
Quantity
Shipping Cost: $0.00