Hausa8

NAUYIN ZUNUBI

$0.04

Tattaunawa mai zurfi game da zunubi, adalci, da jinkai. Yadda Allah ke gafartawa ta wurin Almasihu.

0.00 reviews
Login to rate

Quantity

01

Shipping Cost: $0.00

HausaTractsForeign Tracts

NAUYIN ZUNUBI


Ni, mutumin gabas ta tsakiya ne,

a kullum na kan ji dadin tattaunawa da abokaina
a wannan bangare na duniya.

Wata rana, na ce masu,
ko kun san cewa mutane da yawa sun yi imani cewa,
a rana ta ƙarshe,
Allah zai auna ayyukansu masu kyau a ma’auni a wannan hannun,
ayyukansu na mugunta kuma a ɗaya hannun,
wanda ta haka zai nuna za su shiga
(sama) aljanna ko kuma jahannama?

Sai suka amsa suka ce,
“I, haka ne, amma kai fa,
ba ka yi tunanin hakan ba?”

Na yi shiru,
na ɗan wani lokaci,
daga nan, sai na amsa cewa:

Tun da mutane da yawa sun yi imanin haka,
wannan ya sa na yi tunani mai zurfi,
cewa, idan na sami dukan duniya, amma a ƙarshe na rasa raina
ina amfanin wannan?

Amma bisa ga yawan tunanin da nake yi akan wannan,
yawan damuwar da takan zo mini.

Sai suka ce:
"Me kake nufi?"

Sai na ce:

To, idan Allah zai sa zunubaina akan ma’auni,
zan so in san nauyin kowanne zunubina,
ku fa?
Zan so in san nauyin kowace karya,
da mugun tunani da kuma girman kaina.

Fiye da komai ma,
zan so in san nauyin dukan zunubaina a gaban Allah Mai Tsarki
wanda ba ya son zunubi.

Ba shi kenan ba.
Zan yi mamakin nauyin ayyukana masu kyau,
ganin cewa sun kasa,
domin suna cike da girman kai da lalata,
da son neman yabo daga mutane.


Abokaina sun yi shiru.

Sai ɗaya daga cikinsu ya ce:

"Begenmu yana ga jinkan Allah da alherinsa kawai."

Sai na ce:

Haka yake,
sai mu gode wa Allah domin Shi mai jinkai ne mai alheri kama.

Amma duk da haka,
jinkansa bai ci karo da Tsarkinsa da adalcinsa ba.

Daga nan, sai ɗaya abokin ya ce:

"Na sani Allah zai iya yin komai,
amma ka bayyana yadda Allah zai aiwatar da adalcinsa tare da nuna jinkai a lokaci guda?"

Sai na amsa na ce:

Ga mutane, wannan ba mai yiwuwa bane.
Idan alkali bai hukunta mai laifi ba,
ya nuna jinkai, amma bai yi adalci ba.
Idan ya nuna cikakken adalci,
to bai nuna cikakken jinkai ba.

Amma zai iya nuna cikakken jinkai a lokaci guda kuma cikakken adalci.

Abokaina cike da mamaki suka yi tambaya:

"Ta yaya?"

Daga nan sai na ba su wani misali.

Misali, ace nayi laifi,
wanda hukuncinsa biyan kudi ne mai yawa,
ko kuma zama a gidan (yari) kurkuku,
amma sai alkalin da kansa ya biya kudin.

Ashe, bai nuna jinkai da kuma adalci a lokaci guda ba?

Sai dukansu suka yarda, cewa:

Hakika, ya nuna jinkai da kuma adalci a lokaci guda.


Abokaina sun yi marmarin sanin yadda Allah yayi hakan domin ’yan adam.

Abokaina mutanen gabas,
masu aminci ne wajen tattaunawa
game da al’amura irin waɗannan—
amma wannan tattaunawar ta sa sun gane cewa,
dogara ga ayyuka (kyawawa) nagari hatsari ne.

Ba su yi musu ba cewa su masu zunubi ne,
yanzu suna marmarin su san yadda za su sami ceto.


Littafi yayi bayani:

“Tunda yake an kaddara wa dan adam ya mutu sau ɗaya ne,
bayan haka kuma sai shari’a”
(Ibraniyawa 9:27).

Sai na bayyana musu cewa:
hukuncin zunubi mutuwa ce ta har abada —
ba mutuwa ta jiki kaɗai ba.

To, ta yaya Allah ya ɗauki nauyin wannan dominmu?
Ta yadda ya zama (ɗan adam) mutum.

Wannan shine ainihin abin da Almasihu yayi dominmu.
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda Allah ya kaunaci ’yan adam kwarai.

Ya aiko da Almasihu ya mutu dominmu.

Almasihu da yardarsa ya mutu a madadinmu,
domin duk wanda ya gaskanta da shi,
kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.


Game da Almasihu kuma,
Littafi Mai Tsarki ya ce:

"Shine duk Annabawa suka yi wa shaida,
cewa albarkacin sunansa duk mai gaskantawa da shi
zai sami gafarar zunubai”
(Ayyukan Manzanni 10:43).


Akwai ’yan littatafai masu ɗauke da koyarwar Littafi Mai Tsarki
da kuma shawarwari kyauta a yalwace.
Idan akwai bukata, sai a rubuta zuwa ga wannan adireshi dake ƙasa:


Hausa-8 “The Weight Of Sin”
Free tracts and biblical counsel available by request. Write:

Word Of Truth
P.O. Box 1126, Kaduna, Nigeria.

Related Products

What is the Truth?

What is the Truth?

The Weight of SIN

The Weight of SIN

Do you know the Humble King?

Do you know the Humble King?

How To Know GOD

How To Know GOD

Do you know your ENEMIES?

Do you know your ENEMIES?

KARMA versus KRUPA

KARMA versus KRUPA

Do You Know the Messiah?

Do You Know the Messiah?

Jewish Discovery of a Lifetime

Jewish Discovery of a Lifetime

Why Believe It?

Why Believe It?

When should you think about CHRIST?

When should you think about CHRIST?

When God Knows Your Your Name

When God Knows Your Your Name

What's Life?

What's Life?

U-Turn

U-Turn

Trapped!

Trapped!

Those Guilty Stains

Those Guilty Stains

THIS THING WORKS!

THIS THING WORKS!

They Gambled and Lost! Will You?

They Gambled and Lost! Will You?

The Problem with Patty

The Problem with Patty

I’m Here for a Good Time

I’m Here for a Good Time

The You Don't Know Yet

The You Don't Know Yet

We use cookies

We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy