
NAUYIN ZUNUBI
$0.04Tattaunawa mai zurfi game da zunubi, adalci, da jinkai. Yadda Allah ke gafartawa ta wurin Almasihu.
Quantity
Shipping Cost: $0.00
We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy
$0.04
Ni, mutumin gabas ta tsakiya ne,
a kullum na kan jiย dadin tattaunawaย da abokaina
a wannan bangare na duniya.
Wata rana, na ce masu,
ko kun san cewa mutane da yawa sun yi imani cewa,
a rana ta ฦarshe,
Allah zai auna ayyukansu masu kyau a maโauni a wannan hannun,
ayyukansu na mugunta kuma a ษaya hannun,
wanda ta haka zai nuna za su shiga
(sama) aljanna ko kuma jahannama?
Sai suka amsa suka ce,
โI, haka ne, amma kai fa,
ba ka yi tunanin hakan ba?โ
Na yi shiru,
na ษan wani lokaci,
daga nan, sai na amsa cewa:
Tun da mutane da yawa sun yi imanin haka,
wannan ya sa na yi tunani mai zurfi,
cewa,ย idan na sami dukan duniya, amma a ฦarshe na rasa raina
ina amfanin wannan?
Amma bisa ga yawan tunanin da nake yi akan wannan,
yawanย damuwar da takan zo mini.
Sai suka ce:
"Me kake nufi?"
Sai na ce:
To,ย idan Allah zai sa zunubaina akan maโauni,
zan so in sanย nauyin kowanne zunubina,
ku fa?
Zan so in sanย nauyin kowace karya,
daย mugun tunaniย da kumaย girman kaina.
Fiye da komai ma,
zan so in san nauyinย dukan zunubaina a gaban Allah Mai Tsarki
wanda ba ya son zunubi.
Ba shi kenan ba.
Zan yi mamakinย nauyin ayyukana masu kyau,
ganin cewa sun kasa,
domin suna cike da girman kai da lalata,
da son neman yabo daga mutane.
Sai ษaya daga cikinsu ya ce:
"Begenmu yana ga jinkan Allah da alherinsa kawai."
Sai na ce:
Haka yake,
sai mu gode wa Allah dominย Shi mai jinkai ne mai alheri kama.
Amma duk da haka,
jinkansa bai ci karo da Tsarkinsa da adalcinsa ba.
Daga nan, sai ษaya abokin ya ce:
"Na sani Allah zai iya yin komai,
amma ka bayyana yadda Allah zai aiwatar da adalcinsa tare da nuna jinkai a lokaci guda?"
Sai na amsa na ce:
Ga mutane,ย wannan ba mai yiwuwa bane.
Idan alkali bai hukunta mai laifi ba,
ya nuna jinkai, amma bai yi adalci ba.
Idan ya nuna cikakken adalci,
to bai nuna cikakken jinkai ba.Ammaย zai iya nuna cikakken jinkai a lokaci guda kuma cikakken adalci.
Abokaina cike da mamaki suka yi tambaya:
"Ta yaya?"
Daga nan sai na ba su wani misali.
Misali, ace nayi laifi,
wanda hukuncinsaย biyan kudi ne mai yawa,
ko kumaย zama a gidan (yari) kurkuku,
amma sai alkalinย da kansa ya biya kudin.Ashe, bai nunaย jinkai da kuma adalci a lokaci guda ba?
Sai dukansu suka yarda, cewa:
Hakika, ya nuna jinkai da kuma adalci a lokaci guda.
Abokaina sun yi marmarin sanin yadda Allah yayi hakan domin โyan adam.
Abokainaย mutanen gabas,
masu aminci ne wajen tattaunawa
game da alโamura irin waษannanโ
amma wannan tattaunawar ta sa sun gane cewa,
dogara ga ayyuka (kyawawa) nagari hatsari ne.
Ba su yi musu ba cewaย su masu zunubi ne,
yanzu suna marmarin su san yadda za su sami ceto.
Littafi yayi bayani:
โTunda yake an kaddara wa dan adam ya mutu sau ษaya ne,
bayan haka kuma sai shariโaโ
(Ibraniyawa 9:27).
Sai na bayyana musu cewa:
hukuncin zunubi mutuwa ce ta har abadaย โ
ba mutuwa ta jiki kaษai ba.
To,ย ta yaya Allah ya ษauki nauyin wannan dominmu?
Ta yaddaย ya zama (ษan adam) mutum.
Wannan shine ainihin abin daย Almasihu yayi dominmu.
Littafi Mai Tsarkiย ya gaya mana yaddaย Allah ya kaunaci โyan adam kwarai.
Ya aiko da Almasihu ya mutu dominmu.
Almasihu da yardarsa ya mutu a madadinmu,
domin duk wanda ya gaskanta da shi,
kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.
Game da Almasihu kuma,
Littafi Mai Tsarki ya ce:
"Shine duk Annabawa suka yi wa shaida,
cewa albarkacin sunansa duk mai gaskantawa da shi
zai sami gafarar zunubaiโ
(Ayyukan Manzanni 10:43).
Akwai โyan littatafai masu ษauke da koyarwar Littafi Mai Tsarki
da kuma shawarwari kyauta a yalwace.
Idan akwai bukata, sai a rubuta zuwa ga wannan adireshi dake ฦasa:
Hausa-8 โThe Weight Of Sinโ
Free tracts and biblical counsel available by request. Write:
Word Of Truth
P.O. Box 1126, Kaduna, Nigeria.

Tattaunawa mai zurfi game da zunubi, adalci, da jinkai. Yadda Allah ke gafartawa ta wurin Almasihu.
Quantity
Shipping Cost: $0.00