Hausa2

NINE HANYA

$0.04

Yesu shi kaɗai ne hanyar zuwa sama . Ka zo gare shi yau, ka gaskata, domin ceto yana gare shi kaɗai.

0.00 reviews
Login to rate

Quantity

01

Shipping Cost: $0.00

HausaTractsForeign Tracts

NINE HANYA


Cikin ‘yan kwanakin nan,
kai da ni zamu bar wannan duniya —
mai yiwuwa ne tafiya ta zo da sauri
har fiye da yadda muke zato.

Ka san hanyar zuwa Sama?

Akwai mutane masu mutunci da yawa
wadanda ke zaton zasu iya zuwa sama
ta wurin aikata ayyuka masu kyau,
ko kuma ta wurin rayuwa mai kyau,
ko kuma ta wurin aikin ibada tukuru.

Suna sa ran samun shiga sama,
gidan Allah,
ta wurin aikata ayyuka nagari.
Amma wannan ba hanyar Allah ba ce.

Duk da irin kyaun wadannan abubuwa
da zasu iya aikatawa,
ba su bane hanyar zuwa sama wurin Allah.


Yesu Kristi
shi ne hanyar zuwa sama, gidan Allah.

Yesu ya ce,
“Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai.
Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina”
(Yohanna 14:6).

Zunubi guda ɗaya kaɗai
ya sa Allah ya kawar da Adamu da Hawwa’u
daga Gonar Aidan har abada.

Haka zunubi guda zai rufe maka kofar sama har abada —
sai idan ka dogara ga Yesu Kristi
a matsayin Mai Cetonka.

Ka ba da gaskiya gare shi?
Idan ba ka ba da gaskiya gare shi ba,
me za ya hana ka gaskata yanzun nan?

Shaidan yana rudinka da cewa,
“Ka dan jira kaɗan.”
Allah yana faɗa maka cewa,
“Yau ce ranar ceto” (2 Korintiyawa 6:2).


A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah yana faɗa mana cewa
akwai wurare biyu kawai da mutane
zasu zauna har abada bayan sun bar wannan duniya.

Ɗaya daga cikin wuraren nan shine gidan wuta:

“Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai ba,
sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.”
(Ruya ta Yohanna 20:15)

“Amma... marasa bada gaskiya...
rabonsu yana cikin korama mai ci da wuta da kibiritu;
mutuwa ta biyu ke nan.”
(Ruya ta Yohanna 21:8)

Wadannan ne za su shiga madawwamiyar azaba har abada
(Matta 25:41, 46)
“Cikin wuta marar kasuwa.
A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa,
wutar kuma ba a kashe ta.”
(Markus 9:43–44)


Wurin na biyu da mutane za su zauna har abada
shine wurin da Ubangiji Yesu Kristi yake da zama —
wurin da dukkan waɗanda suka karɓi Kristi a matsayin Mai Cetonsu za su kasance.

“Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.
A gun Ubana akwai wurin zama da yawa.
Da ba haka ne ba, da na faɗa muku.
Domin zan tafi in shirya muku wuri.
In kuwa na je na shirya muku wuri,
sai in dawo in kai ku wurina,
domin inda nake, ku ma ku zama kuna can.”
(Yohanna 14:1–3)

“Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki,
taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.”
(Zabura 16:11)


Lokacin da Yesu yana nan a duniya ya ce:

“Ku zo gare ni, dukanku masu wahala,
masu fama da kayan zunubi,
ni kuwa zan hutasshe ku.” (Matta 11:28)

“Wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.”
(Yohanna 6:37)

Yesu, Mai Ceto wanda ya tashi daga matattu,
a yau yana marmari masu zunubi su zo wurinsa
da kukan zunubansu da kuma bukatunsu,
kamar yadda suka rika zuwa wurinsa lokacin da yake a nan duniya.

Idan kai mai zunubi ne, ka zo wurin Yesu Kristi,
kuma ka bada gaskiya gare shi a matsayin Mai Cetonka,
zaka sami alkawarin Allah:

Zaa gafarta maka zunubanka
(duba Ayyukan Manzanni 10:43)
Kuma zaka je sama gidan Allah kai-tsaye.

YESU NE HANYAR ZUWA SAMA —
babu wata hanya ko kaɗan.
— FE W.C. Wurst

“Gama Allah ya yi kaunar duniya,
har ya bada Dansa makadaici,
domin dukkan wanda yake bada gaskiya gare shi,
kada ya hallaka, amma ya sami rai na har abada.”
(Yohanna 3:16)

Related Products

What is the Truth?

What is the Truth?

The Weight of SIN

The Weight of SIN

Do you know the Humble King?

Do you know the Humble King?

How To Know GOD

How To Know GOD

Do you know your ENEMIES?

Do you know your ENEMIES?

KARMA versus KRUPA

KARMA versus KRUPA

Do You Know the Messiah?

Do You Know the Messiah?

Jewish Discovery of a Lifetime

Jewish Discovery of a Lifetime

Why Believe It?

Why Believe It?

When should you think about CHRIST?

When should you think about CHRIST?

When God Knows Your Your Name

When God Knows Your Your Name

What's Life?

What's Life?

U-Turn

U-Turn

Trapped!

Trapped!

Those Guilty Stains

Those Guilty Stains

THIS THING WORKS!

THIS THING WORKS!

They Gambled and Lost! Will You?

They Gambled and Lost! Will You?

The Problem with Patty

The Problem with Patty

I’m Here for a Good Time

I’m Here for a Good Time

The You Don't Know Yet

The You Don't Know Yet

We use cookies

We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy