
NINE HANYA
$0.04Yesu shi kaษai ne hanyar zuwa sama . Ka zo gare shi yau, ka gaskata, domin ceto yana gare shi kaษai.
Quantity
Shipping Cost: $0.00
We use cookies to ensure you get the best experience on our website. For more information on how we use cookies, please see out cookie policy. Cookie Policy
$0.04
Cikin โyan kwanakin nan,
kai da ni zamu bar wannan duniya โ
mai yiwuwa ne tafiya ta zo da sauri
har fiye da yadda muke zato.
Ka san hanyar zuwa Sama?
Akwai mutane masu mutunci da yawa
wadanda ke zaton zasu iya zuwa sama
ta wurin aikata ayyuka masu kyau,
ko kuma ta wurin rayuwa mai kyau,
ko kuma ta wurin aikin ibada tukuru.
Suna sa ran samun shiga sama,
gidan Allah,
ta wurin aikata ayyuka nagari.
Amma wannan ba hanyar Allah ba ce.
Duk da irin kyaun wadannan abubuwa
da zasu iya aikatawa,
ba su bane hanyar zuwa sama wurin Allah.
Yesu Kristi
shi ne hanyar zuwa sama, gidan Allah.
Yesu ya ce,
โNi ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai.
Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurinaโ
(Yohanna 14:6).
Zunubi guda ษaya kaษai
ya sa Allah ya kawar da Adamu da Hawwaโu
daga Gonar Aidan har abada.
Haka zunubi guda zai rufe maka kofar sama har abadaย โ
sai idan ka dogara ga Yesu Kristi
a matsayin Mai Cetonka.
Ka ba da gaskiya gare shi?
Idan ba ka ba da gaskiya gare shi ba,
me za ya hana ka gaskata yanzun nan?
Shaidan yana rudinka da cewa,
โKa dan jira kaษan.โ
Allah yana faษa maka cewa,
โYau ce ranar cetoโย (2 Korintiyawa 6:2).
A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah yana faษa mana cewa
akwai wurare biyu kawai da mutane
zasu zauna har abada bayan sun bar wannan duniya.
ฦaya daga cikin wuraren nan shine gidan wuta:
โDuk wanda ba a sami sunansa a rubuce a Littafin Rai ba,
sai a jefa shi a tafkin nan na wuta.โ
(Ruya ta Yohanna 20:15)
โAmma... marasa bada gaskiya...
rabonsu yana cikin korama mai ci da wuta da kibiritu;
mutuwa ta biyu ke nan.โ
(Ruya ta Yohanna 21:8)
Wadannan ne za su shiga madawwamiyar azaba har abada
(Matta 25:41, 46)
โCikin wuta marar kasuwa.
A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa,
wutar kuma ba a kashe ta.โ
(Markus 9:43โ44)
Wurin na biyu da mutane za su zauna har abada
shine wurin daย Ubangiji Yesu Kristiย yake da zama โ
wurin da dukkan waษanda suka karษi Kristi a matsayin Mai Cetonsu za su kasance.
โKada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.
A gun Ubana akwai wurin zama da yawa.
Da ba haka ne ba, da na faษa muku.
Domin zan tafi in shirya muku wuri.
In kuwa na je na shirya muku wuri,
sai in dawo in kai ku wurina,
domin inda nake, ku ma ku zama kuna can.โ
(Yohanna 14:1โ3)
โKasancewarka takan sa in cika da farin ciki,
taimakonka kuwa yana kawo jin daษi har abada.โ
(Zabura 16:11)
Lokacin da Yesu yana nan a duniya ya ce:
โKu zo gare ni, dukanku masu wahala,
masu fama da kayan zunubi,
ni kuwa zan hutasshe ku.โย (Matta 11:28)
โWanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaษan.โ
(Yohanna 6:37)
Yesu,ย Mai Ceto wanda ya tashi daga matattu,
a yau yana marmari masu zunubi su zo wurinsa
daย kukan zunubansu da kuma bukatunsu,
kamar yadda suka rika zuwa wurinsa lokacin da yake a nan duniya.
Idan kai mai zunubi ne, ka zo wurin Yesu Kristi,
kuma ka bada gaskiya gare shi a matsayin Mai Cetonka,
zaka sami alkawarin Allah:
Zaa gafarta maka zunubanka
(duba Ayyukan Manzanni 10:43)
Kuma zaka je sama gidan Allah kai-tsaye.
YESU NE HANYAR ZUWA SAMA โ
babu wata hanya ko kaษan.
โย FE W.C. Wurst
โGama Allah ya yi kaunar duniya,
har ya bada Dansa makadaici,
domin dukkan wanda yake bada gaskiya gare shi,
kada ya hallaka, amma ya sami rai na har abada.โ
(Yohanna 3:16)

Yesu shi kaษai ne hanyar zuwa sama . Ka zo gare shi yau, ka gaskata, domin ceto yana gare shi kaษai.
Quantity
Shipping Cost: $0.00